• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ziyarar Shugaban Aljeriya A Kasar Sin Za Ta Karfafa Dangantakar Kasashen Biyu

by CMG Hausa
2 years ago
Aljeriya

LABARAI MASU NASABA

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya isa filin jirgin sama na kasa da kasa na birnin Beijing domin ziyarar aiki ta kwanaki biyar a kasar Sin daga yau Litinin. Wannan dai ita ce ziyarar farko da shugaban na Aljeriya ya kai kasar Sin tun bayan hawansa mulki. 

Da yake tsokaci don gane da ziyarar, shugaban kungiyar raya abota tsakanin Sin da Aljeriya, Isma’il Dabash, ya ce wannan ne karo na farko da shugaban na Aljeriya ya ziyarci kasar Sin tun bayan hawa karagar mulkin kasar, kuma ya yi imanin cewa, ziyarar za ta kara kyautata dangantakar abota dake tsakanin kasashen biyu.

  • Sin Tana Kiyaye Matsayinta Na Zama Ginshikin Ci Gaban Duniya

A cewar Isma’il Dabash, kasar Sin ta taimakawa Aljeriya a shekarun 1950, lokacin da kasar ke fafutukar neman ‘yanci. Yana mai cewa, Sin ce kasa ta farko da ba ta Larabawa ba, da ta amince da kasar Aljeriya. Haka kuma Aljeriya a nata bangare, ta taimakawa Sin matuka, wajen dawo da halaltacciyar kujerarta a MDD. Ya ce shaidu sun nuna cewa Aljeriya da Sin sun kasance masu taimakon juna kuma aminai dake hadin gwiwa.

Bugu da kari, Isma’il Dabash ya ce Aljeriya ta shiga shawarar Ziri Daya da Hanya Daya a shekarar 2018, kuma kasashen biyu sun rattaba hannu kan shawarar a shekarar 2022. Ya jaddada cewa, shigar Aljeriya cikin shawarar ba karfafa hadin gwiwar moriyar juna tsakaninta da Sin kadai zai yi ba, har ma da karawa tattalin arzikinta kuzarin bunkasuwa. (Fa’iza Mustapha, Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya
Daga Birnin Sin

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Next Post
Farfado Da Burin Rage Amfani Da Tsabar Kudi A Tsakanin Al’umma

Lauyoyi 60 Sun Yi Karar DSS Kan Kin Sakin Emefiele

LABARAI MASU NASABA

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025
Gwamnonin Arewa Sun Jajanta Wa Jihar Neja Kan Fashewar Tankar Mai

Gwamnonin Arewa Sun Jajanta Wa Jihar Neja Kan Fashewar Tankar Mai

October 26, 2025
El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

October 26, 2025

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin Bunƙasa Kasuwancinsu

October 26, 2025
Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

October 26, 2025
Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

October 26, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.