Sha’anin kyalayar da jinanan mutane cikin siyasar Nijeriya na da dogon tarihi, faro tun daga lokacin da Turawan Birtaniya ke jan akalar mulkin kasar zuwa yau. A baya bayan, mu dan nazarci sashen wasu kalamai da Dr Muhammad Kuna na Jami’ar Shehu Danfodio da ya yi, game da ta’addancin da ke da nasaba da siyasa shekaru 1b da su ka gabata. Dubi kasa;
“… Da yawan masu nazari game da abubuwan da suke faruwa na tashe-tashen hankulan da ake samu wadanda ke da nasaba da siyasa, na nuna matukar damuwarsu, ta yadda za a ga cewa, a na amfani da irin wadancan rikice-rikice ne a matsayin wata hanya ta kai wa ga samun shugabancin jama’a…
…irin wadancan tada-zaune-tsaye da aka samu cikin wasu ‘yan watanni da suka shude, na nuna irin yadda abubuwa ke kara ta’azzara. An cigaba da samun kashe-kashe da ta’addancin da ke da nasaba da siyasa da kuma rashin bin umarnin kotu…an samu cewa, wasu ‘yan siyasa ne ke daukar nauyin irin wadancan tashe-tashen hankula na siyasa…
…Irin wadannan miyagun ta’adodi da su ke kwarara ko’ina cikin wannan kasa, inda za a ga matasa dauke da sanduna, adduna, wukake, a wasu wuraren ma, za a ga matasan ne dauke da bindigogi. Yanayin da za a ga irin wadancan matasa na yawo waje-waje, suna masu farautar abokanan adawarsu ta siyasa, sai ya tuna maka ne da ‘yan Nazi na kasar Jamus, na shekarun 1920s zuwa 30s…”.
(Daily Trust, April 12, 2007).
Dakta Kuna ya kara da cewa, banbancin tashe-tashen hankula na ‘yan Nazi, da wanda ke faruwa a wannan Kasa tamu, bai wuce cewa, a Jamus, wasu jama’a ne ke shirya tashe-tashen hankulan, don su shafe wata al’uma daga doron kasa. A nan Nijeriya kuwa, za a ga cewa, wasu mutane ne ke shirya irin wadancan rikice-rikice, don kawar da abokanan adawarsu na siyasa daga doron kasa, wanda a tunaninsu, hakan ne kadai zai kai su ga cimma muradunsu.
Dangantar Rikicin Boko Haram Da Siyasa
Kafin gabatar da wasu misalsalai nan gaba da ke tabbatar da irin yanayi na zub da jinanan bayin Allah da ake kan yi tsawon lokaci a wannan Kasa, da sunan rikicin siyasa, wadanda ke afkuwa a lokacin gudanar da zabukan cikin gida, lokacin kamfen, da lokacin babban zabe na Kasa, ta tabbata cewa, akwai ma wasu nau’ikan wasu rikice-rikicen da sai manazarta masana ne ka iya gano hakikanin ababen da su ke haddasar da su, kasantuwar zahirinsu kwata-kwata ya saba da badininsu.
Dr Amaechi M. Nwako, mazaunin kasar Scotland, masani kuma manazarci game da rikice-rikicen ta’addanci da ke gudana a matakin kasa da kasa, ya alakanta tashe-tashen hankulan ‘yan Boko Haram da Siyasa. Daktan, ya hakkake wannan bincike nasa ne cikin wata hira da ya yi da jaridar Sunday Trust, ta watan Yunin Shekarar 2011 (Sunday Trust, June 19, 2011).
Dr Nwako na da ra’ayin cewa, batun aiyukan ta’addanci a Nijeriya, magana ce da za a ce ‘yan siyasa ne ke ba da kwarin gwiwar aikata su. Ya kara da cewa, irin wadancan kungiyoyi da ke haddasa rikice-rikice, da farko, suna yi ne ba da sunan addini ba, sai daga bisani ne suke sanya rigar addini.
Zubar Da Jini A Zabukan Cikin Gida Na Jam’iyya
Ta tabbata cewa, ‘yan siyasa a wannan kasa ta Nijeriya, na sabawa ne da zubar da jinanen junansu, tun daga matakin zabukan cikin gida na jam’iyya “Primary Elections”, gabanin kai wa ga matakin manyan zabuka “Secondary Elections” da za su buga, a tsakaninsu da sauran jam’iyyun adawa.
Ba ya ga jahilci da hadamar mulki, akwai ma karin wasu dalilai ko ace sabubba, wadanda ke jaza kaiwa zuwa ga kyalayar da jinin al’umar kasar da sunan siyasa. Masana, manazarta da sauran masharhanta, sun sha kokawa a mabanbantan lokuta game da cin-kan juna da ke wakana a tsakanin ‘yan siyasar, musamman cikin wannan jamhuriyar siyasa ta hudu da muke ciki.
Shekaru 21 da su ka gabata, an tambayi tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa, O.C.J. Okocha (SAN), game da mawuyacin yanayin da jam’iyyun siyasar wannan kasa su ka tsinci kansu ciki, sai ya amsa kamar haka;
“…’yan siyasa na kashe kansu da kansu yayin da suke gudanar da zabukan cikin gida na jam’iyya…Lokaci ya yi da ya dace ‘yan siyasar su farka daga dogon barcin da suke ciki, ina tsoron ka da su zama su ne matsalar wannan kasa tamu ta Nijeriya…”.
(Tell, September 1b, 2002).
Wadancan kalamai na Okocha ya yi su ne fa shekaru 21 da su ka gabata, to amma har zuwa yau (2023), wane abu ne ya canja a tsakanin ‘yan siyasar, wanda zai nuna maka cewa sun fara nisatar irin waccan mugunyar ta’ada ta farmakar juna, gami da aike juna zuwa ga barzahu? Da daman dalilan da ake gabatarwa na nanikewa wannan tsari na dimukradiyya, bai wuce son kyautatawa dan’adam ba. Sai kuma aka wayigari a na kashe mutane a kan hanyar wanzuwar mulkin na dimukradiyya!!!.
Wace irin dimukradiyya ce ake aiwatarwa ne a Nijeriya? Sai wannan tambaya ta tuna mana da wasu maganganu da marigayi Chief Gani Fawehinmi ya yi, bayan kammala zabukan Shekarar 2003. Ga abinda Ganin ke cewa;
“… Na tashi a wannan safiya cike da bacin-rai game da abubuwan da ke faruwa cikin wannan kasa na zaben du-gari na Shekarar 2003. Babu kokwanto, irin dimukradiyyar da muke yi, kwata-kwata ba ta kan tafarkin daidai. Babu wata gaskiya ko mutuntaka a cikinta. Gabadayan abubuwan da su ka faru cikin wannan zabe na 2003, babu wani abin dogaro na gaskiya a cikinsa…Ga dukkan alamu, makomar wannan kasa ba zai zamto wani mai kyawo ba. Hakika, ina tausayawa talakawan wannan kasa : ina mai bakin cikin cewa, wannan kasa za ta cigaba da zama karkashin ikon mutanen da ke yin katobararsu son ransu, ba tare da yin wata nadama ba. Mutanen da za su mike kafa tare da kwasar ganima da sunan shugabanni, masu yin kudi ta barauniyar hanya. Ga su tsantsar makaryata, wadanda kullum ke feso karairayi tare da neman yaudarar al’uma, na, su yarda da su, wajen mayar da fari baki, sannan kuma a mayar da fari baki. Sai aka wayigari, karya ita ce gaskiya, ita kuma gaskiyar, sai a birkice ta…”.
(The News, May 5, 2003).