Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna damuwarsa kan ƙarancin shiga makarantar boko a wasu sassan jihar, musamman a garin Gajiganna, inda aka samu ɗalibai 90 ne kacal daga cikin jama’ar da ta kai dubu hamsin ke zuwa makaranta.
Don magance wannan matsala, Gwamna Zulum ya amince da bayar da tallafin Naira dubu ɗari uku ga iyayen yaran 90 da aka sanya a makarantar, inda aka ware wa uban kowane ɗalibi ₦250,000, sannan uwa ta karɓi ₦50,000.
- Gwamna Zulum Ya Bai Wa Jami’ar Sojoji Tallafin Naira Miliyan 100
- Ba Ni Da Niyyar Barin APC Zuwa Wata Jam’iyyar — Gwamna Zulum
A yayin ƙaddamar da Makarantar Sakandare ta Addinin Musulunci (Higher Islamic College) a Gajiganna, gwamnan ya jaddada buƙatar ɗaukar matakai na musamman don farfaɗo da ilimi a arewacin Borno.
Haka kuma ya bayyana burin jihar na ba da damar koyar da ɗaliban tsangaya ilimin da zai ba su damar yin fice a duniyar yau, inda kundin karatun waɗannan makarantu ya haɗa ilimin addini da kimiyya, da lissafi, da fasaha da kuma Ingilishi na asali.
Gwamna Zulum ya kuma ƙaddamar da Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Gajiganna, wacce za ta zama cibiyar ci gaba ga ɗaruruwan ɗaliban da ke kammala firamare a garin Gajiganna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp