Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya aike wa majalisar dokokin jihar wasika, inda ya sanar da cire sunan Dakta Ibrahim Yufus Ngoshe daga cikin sunayen Kwamishinonin da ya aike mata.Â
Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
- LEADERSHIP Ta Dage Taronta Kan Illar Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi
- Shin Audu Maikaba Zai Iya Kawo Gyara A Kano Pillars?
Ya ce, gwamnan ya rage adadin mutanen 18 da ya aike wa majalisar zuwa mutane 17 a ranar Juma’a.
Ya ce, za a fitar da cikakken bayani kan matakin cire sunan Ngoshe idan bukatar hakan ta taso.
Idan za a tuna dai a ranar Juma’a 28 ga watan Yulin 2023 ne, gwamna Zulum ya aike da sunan mutum 18 ga majalisar dokokin jihar ciki har da Ngoshe domin neman tantance su a matsayin wadanda za a yi wa mukaman kwamishinoni.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp