Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da fara amfani da harabar makarantar Sakandare ta gwamnati a matsayin filin wucin gadi domin kaddamar da sabuwar kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya (FCE) a karamar hukumar Gwoza ta jihar.
Makaranatar ta kasance acikin yankin wasu al’umma ne da ke cikin garin Gwoza, a karamar hukumar Gwoza.
Sabuwar cibiyar ita ce irinta ta farko a jihar Borno tun bayan da aka kirkiro jihar a shekarar 1976. Yawancin Jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja na da Jami’ar Tarayya, Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da Kwalejin Ilimi ta Tarayya a jihohin, amma Jihar Borno ta kasance ba ta da Kwalejin Kimiyya da fasaha da Kwalejin Ilimi ta tarayya har sai da gwamnatin Buhari ta kafa su a kwanan baya.
Gwamna Zulum, ya kaddamar da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya a Monguno a kwanan baya, yanzu haka ya sake kaddamar da Kwalejin Ilimi ta Tarayya a Gwoza.