Da misalin karfe 10 na daren jiya Juma’a, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kai ziyarar ba-zata a wasu asibitoci guda biyu da ke Maiduguri.
A yayin ziyarar ya tarar da marasa lafiya a cikin duhu sakamakon rashin wutar lantarki wanda jihar ta dade tana fama da shi.
- Gwamna Zulum Ya Bayar Da Umurnin Cafke ‘Ƴan Bangar Siyasar Borno
- Zulum Ya Nemi Afuwar Atiku Kan Harin Da Aka Kai Wa Tawagarsa A Borno
Asibitocin da Gwamna Zulum ya kai ziyarar sun hada da Asibitin Umaru Shehu Ultra Modern Hospital da Fatima Ali Sheriff Maternity Hospital, da ke unguwar Bulumkutu a birnin Maiduguri.
Gwamnan ya yanke shawarar kai wannan ziyarar ba-zata a asibitocin kai-tsaye, jim kadan da saukarsa filin jirgin birnin Maiduguri.
Gwamnan ya duba yadda abubuwa ke gudana a asibitocin da kansa tare da tabbatarwa idonsa halin da marasa lafiya ke zaman jinya a cikin duhu saboda rashin wadatar man gas wanda injinan bayar da wutar lntarki ke amfani da shi.
Wadannan asibitocin sun dogara ne da injinan wajen samar da wutar lntarki sakamakon yadda Boko Haram suka lalata layukan wutar a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, lamarin da ya tilastawa birnin zama cikin duhu sama da shekara daya.
Zulum ya zanta da ma’aikatan da ke kula da injinan bayar da wutar lantarki a asibitocin, ya kuma tabbatar da cewa babu wata matsala ko kadan, face kawai rashin man gas.