Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba kayan abinci ga magidanta 18,000 a garin Dikwa, bayan da tsuntsaye da wasu ƙwari suka lalata gonakin jama’ar yankin ke dogaro da su wajen rayuwa. An gudanar da rabon ne a ranar Litinin a harabar fadar Shehun Dikwa.
Zulum ya bayyana cewa wannan mataki ya zama dole domin rage raɗaɗin fari da kuma kwari da suka lalata amfanin gona, lamarin da ya bar iyalai da dama ba tare da wadataccen abinci ba. Ya ce duk da cewa gwamnati ta rage rabon tallafin jin ƙai da kashi 90 cikin 100 ba, saboda ingantuwar tsaro da noma da jama’a suka yi, halin da ake ciki a Dikwa ya tilasta ɗaukar matakin gaggawar don kauce wa matsalar yunwa.
- Zulum Ya Tabbatar Da Harin Boko Haram Ya Ci Rayukan Mutane 63
- Gwamna Zulum Ya Bai Wa Jami’ar Sojoji Tallafin Naira Miliyan 100
Baya ga tallafin abinci, gwamnan ya kuma raba sama da Naira miliyan ₦350 ga mata 35,000 a garin. Kowacce mace ta samu Naira 10,000 da zani, yayin da magidanta suka samu buhuna biyu na shinkafa da dawa.
Gwamna Zulum, tare da manyan jami’an gwamnati da suka raka shi, ya tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa harkar noma da kuma samar da ingantattun hanyoyin yaƙar kwari domin kare amfanin gonar manoma a nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp