Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, ya soke lasisin hanyar layin Dogo mallakar hukumar sufurin jiragen kasa.
Wannan umarnin na Zulum, na kunshe cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Isah Gusau ya fitar a jihar.
Zulum, ya dauki matakin ne, saboda aikata ayyukan laifi da wasu mutane suka yi a hanyar ta layin Dogon.
Kazalika, Zulum ya ce, ya fahimci cewa, gwamnatin jihar ce ta amincewa hukumar ta jiragen kasa da ta yi amfani da hanyar ta layin Dogon, amma abin takaici, an bayar da wajen haya, inda wasu na amfani da hanyar don aikata manyan laifuka a wajen.
A cewarsa, bisa wannna dalilin, gwamnatinsa ta soke lasisin domin kasar, mallakar gwamnatin jihar ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp