Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya sha alwashin gyara wa da faɗaɗa sansanin horas da matasan maus yi wa ƙsa hidima (NYSC) na dindindin a jihar.
Da yake karɓar babban Daraktan NYSC, Birgediya Janar Yusha’u Ahmed a Maiduguri, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta gaggauta gina sansanin dindindin domin karɓar ƙarin ‘yan bautar ƙasa. Ya kuma yaba da gudunmawar da likitoci da malaman kimiyya ke bayarwa a makarantu.
- Sin Ta Yi Bikin Tunawa Da Wadanda Aka Hallaka Yayin Kisan Kiyashin Birnin Nanjing
- Tinubu Ya Amince Da Naira Biliyan 80 Domin Sake Gina Madatsar Ruwa Ta Alau Da Ke Borno
Shugaban NYSC ya gode wa gwamnatin Borno bisa tallafin da take bai wa ‘yan bautar ƙasa, ciki har da alawus na musamman, da abinci, da motocin aiki.