Kididdigar da hukumar kula da musayar kudaden kasar Sin ta fitar, ta nuna cewa, zuwa karshen watan Fabarairun shekarar nan ta 2025, yawan musayar kudaden da aka adana na Sin, ya kai dalar Amurka tiriliyan 3.2272, adadin da ya karu da dalar Amurka biliyan 18.2, sama da na karshen watan Janairu, wato karuwar kaso 0.57 cikin dari.
Wani jami’i mai aiki a hukumar kula da musayar kudaden kasar Sin, ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da tushe mai inganci, da fa’ida mai yawa, da juriya mai karfi, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da daidaiton ma’aunin musayar kudaden da aka adana. (Safiyah Ma)














