Ƴan asalin jihar Katsina a ƙarƙashin ƙungiyar Katsina Security Community Initiative (KSCI) sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su fito da sabon tsari domin kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga da ta addabi jihar.
Katsina ta ci gaba da fuskantar hare-haren ta’addanci inda ƴan bindiga ke mamaye ƙauyuka, suna kashe jama’a da yin garkuwa da su don neman kuɗin fansa. Wannan lamari ya tilasta ɗaruruwan mutane barin gidajensu, wasu kuma sun shiga yarjejeniyar sulhu da ƴan ta’adda domin tsira.
Shugaban KSCI, Dr. Bashir Kurfi, ya bayyana a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja cewa kashe-kashen da sace mutane na ƙara tabbatar da cewa dabarun da ake amfani da su yanzu sun kasa magance matsalar. Ya ce fiye da rabin ƙananan hukumomin jihar suna hannun ƴan bindiga, lamarin da ya sa tafiye-tafiye cikin jihar ya zama hadari.
Haka kuma, shugaban ƙaramar hukumar Safana, Abdullahi Sani Safana, ya ce yankinsa ya samu ɗan sassauci sakamakon tattaunawa da shugabannin al’umma da na addini, amma ya nuna damuwa cewa maƙwabtansu da ba su ɗauki irin wannan mataki ba suna kawo tarnaki ga ci gaba.
A nasa ɓangaren, Farfesa Usman Yusuf Bugaje ya gargadi gwamnati cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, matsalar za ta iya bazuwa zuwa manyan birane a jihar.
A ƙoƙarin gwamnati, rundunar sojin Nijeriya ta sanar da shirin kafa sabuwar bataliya a ƙaramar hukumar Malumfashi domin ƙarfafa yaƙi da tashe-tashen hankulan ƴan bindiga a jihar Katsina.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp