Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantar Family Support Programme wato Family Support Programme Old Students Association (FASPOSA) ajin 2018 ta shirya taron lakcoci daban-daban ga ɗalibai sama da guda 100 ‘yan makarantar.
Taron ya gudana ne a babban ɗakin taron makarantar kuma ya samu halartar wasu daga cikin malamai, mambobi da shugabannin ƙungiyar, har ma da manyan baƙin da suka zo daga wajen makarantar.
- Tukunyar Gas Ta Yi Bindiga, Ta Yi Ajalin Wata Mata A Kwara
- “CBN Na Da Goyon Bayana Wajen Sauya Fasalin Naira” —Buhari
Taken taron mai suna ‘CHANGE THE WORLD’ wato ‘A CANZA DUNIYA’ ya samo asali ne bisa irin yadda matasa masu tasowa suke da muhimmiyar rawa wurin canza duniya.
Batutuwan da aka yi lakca akan su sun haɗa da; muhimmancin sana’a a ƙarni na ashirin da ɗaya, illar shaye-shaye da kuma rashin maida hankalin ɗalibai a makarantun Sakandare.
Daga bisani kuma, an gabatar da wasannin kwaikwayo tare da rubutattun waƙoƙin harshen Turanci masu nishaɗantarwa, wa’azantarwa, ilimantarwa da ƙayatarwa.
Da yake jawabi a lokacin taron, shugaban ƙungiyar Auwal Ibrahim, ya bayyana cewa an shirya wannan taron wayar da kai ga daliban domin ilimantar da su akan illar shan miyagun ƙwayoyi, illar satar jarabawa da yadda za su koyi sana’o’i domin dogaro da kansu.
Ya yi kira ga dukkan daliban da su ƙaurace tare da nisantar dukkanin wani nau’in kayan maye saboda hakan ka iya sa rayuwarsu cikin halin ƙaƙani’kayi da lalacewar rayuwa, saboda hakan domin ganin sun inganta rayuwa to tabbas su tabbatar sun guji tare da nisantar kayan maye.
Domin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi babu abin da yake jaza wa sai lalata rayuwa.
Mataimakiyar shugaban kungiyar, Maryam Aminu Saulawa a jawabin da ta yi kira ga dalibai musamman mata akan muhimmancin ilimin ƴaƴa mata, inda ta jawo hankalinsu da su maida hankali akan karatunsu domin ganin sun cimma gaci a rayuwarsu ta nan gaba.
Ta yi kira ga ƴaƴa mata da su kuma tashi su nemi sana’a musamman ƙananan sana’o’i irin wanda mata ke iyayi a cikin gida ba tare da sun bar gidajen iyayansu ba, domin hakan zai taimaka wa rayuwar wajen ganin cewa sun dogara da kansu.
Wakilin shugabar makarantar malam Abubakar Sa’idu, ta nuna jin daɗinta bisa yadda daliban suka cimma nasara a rayuwarsu, da ya sanya suka waiwayo ƙannensu domin bada gudunmawarsu ga ci gaban makarantar.
Abubakar Sa’idu, ya ce makarantar tana alfahari da su kan wannan kyakkyawan aiki da suke yi, sai ya buƙace su da su ɗore da hakan domin cibgaban ilimi a makarantar da Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya, da kuma samar da al’umma tsaftatacciya.
A jawabinsu daban-daban uwar ƙungiyar Misis Fatima Abdullahi da Misis Hajara Korau da kuma malam Musa Umar sun jinjina wa tsofaffin daliban a bisa shirya wannan taro, inda suka bayyana cewa abubuwan da suka tattauna ya yi dai-dai da matsalolin da ake fuskanta a Jihar Katsina, wanda ake buƙatar gudunmuwar kowa a kan haka.
A jawabin skataren ƙungiyar, Sulaiman Nasir shi ma yayi kira ga daliban maza da mata da su maida hankali a karatunsu kuma su ƙauracewa duk wata hanya da ka iya jaza musu satar amsa a lokacin jarabawa, saboda hakan babbar illa ce ga ɗalibi mai neman ilimi.
Sakataren ƙungiyar ya kuma kara da cewa su tashi su nemi sana’a musamman maza, inda ya ce za su iya fara koyon aikin hannu misali: kafinta, kanikanci, fenti, gyaran wutar lantarki da dai sauransu, tun daga yanzu, wato tun suna da ƙuruciyarsu domin hakan zai taimaka musu, da kuma inganta rayuwarsu a shekaru masu zuwa.
Abdulrahman Ibrahim Hassan, jami’in hulda da jama’a na ƙungiyar, ya ce wannan shi ne karon farko da wannan ƙungiya ta shirya irin wannan taro domin ci gaban ɗalibai, ya kuma kara da cewa “In sha Allahu za mu ci gaba da aiwatar da dukkan kyawawan abubuwa ire-iren waɗannan domin ci gaban ɗalibai da matasa har ma da sauran al’umma.”
Daga ƙarshe, malamai da hukumar makarantar sun nuna jin daɗinsu akan irin wannan ci gaba da tsofaffin ɗalibanta suka kawo, sun kuma yi godiya tare da jaddada goyon bayansu akan dukkan abubuwa irin waɗannan.