Bayan rasuwar Ifeanyi, dan fitaccen mawakin Nijeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido, jam’iyyar PDP reshen Jihar Osun ta dakatar da harkokin siyasa na tsawon mako guda.
Wata sanarwa da shugaban riko na jam’iyyar na jihar, Dokta Adekunle Akindele ya raba wa manema labarai a Osogbo a ranar Talata, ta umarci dukkanin sassan jam’iyyar da kwamitoci da su dakatar da ayyukansu domin jajantawa iyalan Davido.
- Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Makarantar ‘Family Support Programme’ Ta Shirya Taron Lakcoci Ga Ɗalibai Sama Da 100 A Katsina
- Ganduje Ya Kaddamar Da Manyan Motocin Sufuri 100 Da Kanana 50 A Kano
A cikin sakon ta’aziyya ga iyalan Adeleke, Dakta Akindele ya bayyana lamarin a matsayin wani lamari mai ban tausayi.
“Muna jimamin mutuwar danmu Ifeanyi, muna addu’ar Allah ya jikansa, wannan rana ce ta bakin ciki amma mun mika lamarinmu ga Ubangijin talikai.
“Muna mika ta’aziyyarmu zuwa ga Davido, jakadan matasanmu, muna mika ta’aziyya ga mahaifinmu, Dokta Deji Adeleke da dukan dangin Adeleke.
“Muna addu’ar Ubangiji ya bai wa iyalan ikon jure wannan rashi nasu,” in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp