Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta cafke wasu matasa a yankin Sheka bayan ɓarkewar rikici tsakanin ƙungiyoyin ƴan daba.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, yana mai cewa rikicin ya fara ne bayan mutuwar wani matashi mai suna Yusuf Aminu, ɗan unguwar Sheka Babban Layi, wanda ake zargi da aikata fashi da sauran laifuka.
- Dabaru Irin Na Sin A Kan Daidaita Harkokin Duniya A 2024
- An Yi Taro Don Tattauna Dabarar Aiwatar Da Shawarar Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya A MDD
Rahotanni sun nuna cewa marigayin mamba ne na ƙungiyar ‘Yan Shida,’ wacce ta addabi yankin Sheka da aikata fashi da tashin hankali. Wasu mazauna unguwar sun kama shi, suka kakkarya masa ƙafa tare da jikkata wasu, wanda hakan ya kai ga mutuwarsa.
Bayan faruwar lamarin, abokan marigayin suka yi ɗamarar ɗaukar fansa, lamarin da ya janyo rikici mai muni a yankin. Sai dai ‘yansanda sun yi gaggawar shiga tsakani, suka kama wasu daga cikin matasan tare da maido da doka da oda a yankin.