Rundunar Ƴansanda a jihar Katsina ta tabbatar da harin ‘yan bindiga a garin kukar Babangida da ke ƙaramar hukumar Jibia inda suka sace mutane 7 sannan suka ƙona mota kirar J5.
Kakakin rundunar Ƴansanda ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai a Katsina
- Mangal Ya Dauki Nauyin Yi Wa Masu Ciwon Mafitsara 80 Aiki A Katsina
- Jihar Katsina Ta Kafa Kwamitin Rabon Shinkafar Da Tinubu Ya Bayar
Ya ce a jiya Asabar ne ƴan bindigar ɗauke da muggan makamai irin su bindiga kirar AK 47 suka tare gadar kukar Babangida a kan hanyar magana zuwa Katsina inda suka tare mota kirar J5 suka sace mutun 7 a cikin ta sannan suka ƙona motar.
Sanarwar ta ce, Baturen Ƴansanda na ƙaramar hukumar Jibia bai tsaya wata-wata ba inda ya shirya jami’an tsaro tare da haɗin gwuiwar dakarun tsaron gwamna Radda C-Watch da kuma ƴan banga suka tunkari wajen da abin ya faru.
“Bayan isar jami’an tsaro wajen da abin ya faru, sun yi nasarar fatatakar ƴan bindigar tare da kuɓutar da duk mutanen da aka yi garkuwa da mutum bakwan” inji sanarwar
Sai dai kuma sanarwar ta ce mutum ɗaya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su ya samu rauni a kafada a lokacin ɗauki ba daɗin wanda aka hanzarta kai shi asibiti inda yanzu haka yana karɓar magani.
Haka kuma kakakin rundunar Ƴansanda ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce ana cigaba da ƙoƙarin ganin an kama waɗanda suka aikata wannan laifin domin gurfanar da su a gaban kuliya manta sabo.