Ɗan wasan gaba na Super Eagles, Umar Sadiq, zai koma ƙungiyar Valencia a matsayin aro daga Real Sociedad a watan Janairu.
Bisa bayanan kwararren mai harkokin sauya sheƙar ƴan wasa, Fabrizio Romano, an riga an kammala yarjejeniyar, kuma Sadiq zai yi gwajin lafiyarsa a Valencia ranar Jumma’a. Romano ya bayyana cewa yarjejeniyar ta haɗa da zaɓin siyan ɗan wasan nan gaba.
- Shin Ahmed Musa Zai Iya Dawowa Da Rigarsa A Super Eagles Kuwa?
- Kayayyakin Agaji Na Gaggawa Na Kasar Sin Sun Isa Vanuatu
Tun bayan komawarsa Real Sociedad daga Almería, Sadiq ya samu ƙalubalen samun dama ta dindindin. Ya yi gogayya da ƙungiyoyin Valencia, Sevilla, da Getafe a bazarar da ta gabata. A gefe guda, ya ci kwallaye huɗu tare da taimaka wa a ci ƙwallo sau biyu a wasanni 50 da ya yi wa Real Sociedad.