Ƙanin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya shigar da kara a gaban kotu domin ta hana Gwamna Abba Kabir Yusuf, daukar mataki a kan wani fili da ake dambaruwa a kansa.
Kamar yadda bayanin da kunshe cikin karar har da hukumar KNUPDA da Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano da sauran wasu mutane.
- Firaministan Kasar Sin Ya Jagoranci Taron Majalisar Gudanarwar Kasar Sin
- Makarantu Masu Zaman Kansu Sun Koka Kan Kudaden Tafiyar Da Ayyukansu
Shi dai wannan filin Kwankwaso ne ya bai wa wani kamfani mai suna WAECO, amma sai Gwamna Abdullahi Ganduje ya kwace filin bisa wasu dalilai.
Daga baya sai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta tabbatar da kwace filin, wanda ya ke a rukunin gidaje na Kwankwasiyya City, bisa hujjar cewa lokacin da suka bayar da filin ga kamfanin WAECO bai yi rijistar zama cikakken kamfani ba.
Bayan daukar wancan mataki ne kuma sai Ganduje ya dawo da kasuwar ‘yan magani cikin wani bangare na filin.
Shi ma Abba da ya hau mulki, sai ya ƙi mayar wa kamfanin WAECO filin, shi ne Garba Kwankwaso ya shigar da kara.
A umarnin da ya bayar, Mai Shari’a Usman Na’abba ya bayar da umarnin hana taba filin ga Gwamnati, sannan ya dage sauraren koken zuwa 27 ga watan Nuwambar Shekar Da ake ciki.