Wani Ƙasurgumin Ɗan Fashi da makami mai suna Halifa Baba-Beru ya rasu bayan wata arangama da jami’an rundunar ‘yansandan jihar Kano a ranar Talata.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Laraba, ta ce ta samu kiran waya da misalin karfe 1:00 na dare a ranar 22 ga Afrilu, 2025, cewa, wata tawagar ‘yan fashi da makami karkashin jagorancin Baba-Beru, ta far wa mazauna unguwar Gwammaja da ke karamar hukumar Dala ta jihar.
- Yanzu-yanzu: Gwamnan Delta Oborevwori Ya Fice Daga PDP Zuwa APC
- Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan, SP Haruna Kiyawa, jami’an ‘yansandan sun yi artabu da ‘yan fashin a lokacin da suka isa wurin, jami’ai biyu – Kofur Abdullahi Ibrahim da Sajan Yahaya Saidu, sun samu raunuka.
Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban tawagar ‘yan fashin, Baba-Beru ya samu munanan raunuka, wanda daga baya ya rasu a Asibiti.
“An garzaya da dukkan wadanda suka samu raunuka zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda Baba-beru ya rasu a lokacin da ake jinyarsa, amma jami’an ‘yansanda an sallame su bayan sun gama jinya,” in ji sanarwar.
Rundunar ‘yansandan ta ce Baba-Beru, mazaunin Kofar Mazugal a karamar hukumar Dala, na cikin jerin sunayen wadanda ake nema ruwa a jallo kafin faruwar lamarin.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, ya yabawa bajintar jami’an da suka dakile yunkurin ‘yan fashin tare da jaddada aniyar rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi ko su bayar da bayanan da za su kai ga kama wadanda ake zargin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp