Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta roki kungiyoyin kwadago na Nijeriya NLC da TUC da su dakatar da shiga yajin aikin da suke shirin yi domin amfanin ‘Yan Nijeriya.
Mista Pedro Obi, Shugaban NANS na kasa, ya yi wannan roko a wani taron manema labarai a Abeokuta ranar Asabar.
- Rashin Cika Alkawari: ASUU Na Gangamin Shiga Wani Sabon Yajin Aiki
- Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Bayan An Farmake Su Bisa Zargin Sakaci Da Aiki A Ekiti
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa NLC da TUC a ranar 8 ga watan Fabrairu sun fitar da sanarwar yajin aikin na tsawon kwanaki 14 ga gwamnati kan rashin aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma a ranar 2 ga watan Oktoba, biyo bayan cire tallafin man fetur.
Obi, ya bayyana cewa kungiyar ta yi tarayya cikin radadin da ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman matasa da dalibai kan halin kuncin da ake ciki.
Ya bayyana cewa kungiyar na da yakinin cewa yajin aikin da aka shirya idan aka fara shi zai kara dagula tabarbarewar tattalin arzikin kasar.
Shugaban NANS, ya kara da cewa kungiyoyin kwadagon na da ‘yancin gabatar da bukatu tare da shiga yajin aiki ba, ya roki a sake duba wannan matakin.
Ya bukace su da su yi la’akari da illar da ka iya haifar da rashin tsaro, tattalin arziki da kuma mafi mahimmanci, ci gaban karatun dalibai a fadin kasar nan.