Kungiyar Likitoci na asibitin koyarwa na jami’ar jihar Ekiti (EKSUTH) ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani kan harin da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai a asibitin.
An rahoto cewa, ‘yan daban sun kai farmaki asibitin ne a ranar Litinin bayan mutuwar wani mara lafiya da aka kawo asibitin a ranar Lahadi.
- Kano: Sanusi Lamido Ya Soki Gawuna Kan Rashin Karɓar Faɗuwa Zaɓe A Karon Farko
- Yadda Tsohon Minista Ya Jagoranci Tattara Naira Miliyan 50 Kudin Fansa Ga ‘Yan Matan Da Aka Sace
Acewar wata majiya, an kawo majinyacin asibitin ne a wani hali mawuwaci inda hakan yasa aka ajiye shi a sashin bayar da agajin gaggawa na asibitin amma duk da haka ya ce, ga garinku nan, ba a iya ceto rayuwarsa ba.
Rasuwar majinyacin ce ta fusata ‘yan uwansa, inda suka gayyato ‘yan daba suka farmaki likitocin tare da lalata dukiyoyi a asibitin saboda zargin da suka yi wa likitocin na sakaci da aiki.
An tura jami’an rundunar ‘yansandan jihar zuwa asibiti domin dawo da zaman lafiya da tsaron dukiyoyi amma dai kungiyar likitocin a zaman da ta yi na gaggawa, ta yanke hukuncin tsunduma yajin aiki, inda ta ce, “ana barazana ga lafiyar mambobinta”