Kungiyar Shugabannin Matasan Arewa (NNYLF), ta gargadi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da dan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore, da su janye kudirinsu na fafutukar ganin an fito shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da ake tsare da shi.
Matasan sun ce, ba za su tsaya su sa ido kan yadda Atiku da Sowore, suke son yin amfani batun fito da shugaban masu fafutukar Biafra ba, wajen kaddamar da yakin neman zabe da ka iya cinna wa kasar wuta. A maimakon haka, su jira su bai wa kotu damar bincikar shari’ar ta’addancin da ake yi wa shugaban na IPOB.
- Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci
- Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya
Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Murtala Muhammed Gamji, ya bayyana matsayin kungiyar a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata a Abuja, inda suka bayyana shirinsu na gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga sauye-sauyen da shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu yake kawo wa na ci gaban wannan kasa, wanda zai fara daga ranar 20 ga watan Oktoban 2025.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bi sahun dan rajin kare hakkin dan adam kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, wajen yin kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin jagoran kungiyar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na D, Atiku, ya bayyana ci gaba da tsare Kanu a matsayin “rashin girmama bin doka a Nijeriya.”
Kanu dai, na fuskantar tuhumar ta’addanci ne da cin amanar kasa da kuma nuna tunzura a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, wanda kuma a lokuta da dama yake musanta hakan. Har ila yau, ya kasance a tsare tsawon shekaru duk da hukuncin da kotu ta yanke na bayar da umarnin a sake shi.
Atiku, tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya bayyana cikakken goyon bayansa da fafutukar da Sowore ke yi na ga nin an saki Kanu.
Da yake yin jawabi a wajen taron, Kwamared Gamji ya bayyana cewa; “Mun zo nan ne, domin mu nuna fushinmu da rashin amincwar mu da kuma nuna wa duniya cewa, ba ma tare da ‘yan siyasa masu neman mulki ido rufe a Nijeriya, wadanda ke son yin amfani da tsare Nnamdi Kanu wajen tayar da zaune tsaye a kasar.
“Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma mamallakin gidan jaridar Sahara Reporter, Mista Omoleye Sowore, da babanmu, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, na shirin shirya wani gangamin taro, domin sakin Nnamdi Kanu.
Ya kara da cewa, mun ji wannan sanarwa tasu, sannan kuma ba ma tare da su. “Saboda son rai irin naku, kuna so ku yi amfani da jinin matasan Nijeriya, wajen cimma burinku,” in ji Gamji.
“Babban kuskuren da za su tafkawa shi ne, ranar da za su fito, ita ce ranar da matasa sama da miliyan 63, wadanda jiga-jigan matasan Arewa ne; su ma za su fito tare da rokon Shugaba Ahmed Bola Tinubu, da ya ci gaba da gudanar da kyawawan ayyukan da sanya a gaba.
Kwamared Gamji ya kara da cewa, “Za mu mamaye dukkannin titunan Abuja, daga ranakun 20, 21 zuwa 23 ga watan Oktoba, domin nuna goyon bayanmu ga Shugaba Tinubu”.