ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

by Rabi'u Ali Indabawa
10 months ago
Bayelsa

Rundunar ‘Yansandan Jihar Bayelsa ta fara bincike kan bacewar wani dan NYSC mai shekara 24, Mista Lebi Anyanwu, mai lambar rajista BYS/25A/0244, wanda aka bayyana a matsayin wanda ya bace a jihar.

PUNCH Metro ta samu tabbaci daga wata sanarwa a ranar Litinin cewa jami’an Sashen Yaki da Garkuwa da Mutane na rundunar sun kaddamar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.

  • Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi
  • Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

An ruwaito cewa Anyanwu, wanda ake aikinsa na farko a Ijaw National Academy, Kaiama, hedikwatar Karamar Hukumar Kolokuma/Opokuma ta jihar, ya bace tun ranar 8 ga Oktoba, 2025.

ADVERTISEMENT

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Mista Musa Mohammed, ya fitar, rundunar ta umurci Sashen Yaki da Garkuwa da Mutane da su dauki matakai na gaggawa don gano da mayar da dan NYSC din.

Sanarwar ta bayyana cewa an yi zaton yana tare ne da wasu mambobin cocin Jehobah’s Witnesses, Mista da Matarshi Wisdom George, amma su suka ce da fari yana tare da su, sai dai ya tafi daga bisani.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

A cewar ‘yansanda, “A ranar 10/10/25, an gayyato wani Mista Oke Emmanuel, dan NYSC kuma abokin dakin wanda ya bace, domin yi masa tambayoyi. Ya tabbatar cewa wanda ake nema ya kasance tare da iyalan George har zuwa 06/10/25.

“An samu karin bayani daga George cewa dan NYSC din ya koka da rashin lafiya, aka kai su Asibitin Kaiama Referral Hospital a ranar 04/10/25, kuma aka sallame shi ranar 05/10/25. Sai dai a ranar 06/10/25, dan NYSC din ya bace zuwa wani wurin da ba a sani ba.”

‘Yansanda kuma suna binciken zargin karbar kudin rashawa na Naira 100,000 daga iyayen wanda ya bace, da wasu fursunoni biyu da ke gidan gyaran hali na Igbara, Abeokuta, Jihar Ogun, wadanda suka yi suna kamar masu garkuwa da mutane.

“An bar wayar salula ta wanda ya bace a dakinsa. Jami’an bincike suka bi layin kira daga lambar 0906193291, inda aka gano tana hannun wani fursuna da ake tsare da shi a cibiyar gyaran hali ta Igbara, Abeokuta, saboda wani laifin garkuwa da mutane.

“Wanda ake zargin ya ce sun ga lambar wayar a kafafen sada zumunta, suka yi amfani da ita don cutar da mahaifin wanda ya bace, Mista Anyanwu Simon, mai shekara 56. An biya kudin Naira 100,000 zuwa asusun Opay mai lamba 7042793493 na wata Atinuke Oluwalose, abokiyar hadin bakin fursunan da ke gidan yarin Abeokuta.”

“Daga bayanan da jami’an bincike suka gano, akwai wasu abubuwan damuwa da ka iya kasancewa silar abin da ya faru. An gano wasu kalaman da wanda ya bace ya yi dangane da wasu sabbin dabi’u da sha’awowi da ba su dace da akidar addininsa ba,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kammala da cewa ana ci gaba da daukar matakan bincike “domin tabbatar da sakamakon da jami’an bincike suka tattara, kasancewar binciken ya fito da abubuwa masu ban mamaki. Ba a samu wata alamar garkuwa da mutane a wannan lamari ba. Ana ci gaba da aiki domin samun cikakken bincike.”

PUNCH Metro ta ruwaito a watan Oktoba 2024 cewa an kama mutum hudu kan bacewar wani dan NYSC mai suna Yahya Faruk, wanda yake hidima a Ikuru, cikin Karamar Hukumar Andoni ta jihar.

Bayelsa
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Bayelsa

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Bayelsa

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.