Kungiyar wakilan gidajen jaridu na ƙasa reshen jihar Kaduna ta naɗa Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kaduna, Alhaji Sani Liman Kila, a matsayin uban Ƙungiyar.
Da yake jawabi a wajen taron nadin da ya gudana a ofishin Shugaban Ma’aikatan a Fadar Gwamnatin Jihar Kaduna, shugaban kungiyar wakilan ‘Yan Jaridar, Alhaji Abdulghaffar Alabelewa, ya ce la’akari da irin kauna da gudummuwa da Sani Kila ke ba ‘yan jarida a faɗin jihar ne ya sanya kungiyar ta karrama shi da mukamin uban Ƙungiyar.
- NNPCL Ya Bayyana Ranar Da Matatar Man Fetur Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki
- Binciken Gwamnatin El-Rufai: Ko Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Za Ta Rusa Mai Rusau?
Shugaban ‘yan jaridar ya ƙara da cewar ‘yan jarida a Jihar Kaduna a yanzu suna gudanar da ayyukansu cikin walwala da natsuwa saɓanin yadda abubuwa suke a baya inda ya bayyana hakan a matsayin kokari na shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin.
A jawabinsa, Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin, Alhaji Sani Liman Kila, ya godewa Ƙungiyar ‘yan jaridar bisa ga wannan karramawa da suka yi masa, inda ya bayar da tabbacin yin aiki kafada da kafada da su.
“ ‘Yan jarida mutane ne masu muhimmanci a cikin al’umma, wannan karramawa da suka yi mun ta zama abin alfahari a gare ni kasancewa ni ne mutum na farko da ya samu irin wannan matsayi, ina baku tabbacin kofofinmu za su kasance a buɗe gare ku a kowane lokaci”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp