A ranar Lahadi, ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Karongi da ke cikin ƙaramar hukumar Baruten ta jihar Kwara. Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutum 1 da ƙona wasu gidaje da dama.
Ana zargin maharan sun yi amfani da rashin gurbin Ƴansanda waɗanda suka tafi bikin Sallar Layya ƙauyen. Daga baya an kori maharan ne ta hanyar haɗin gwuiwar Sojoji da Ƴansanda daga makwabtan ƙauyuka.
- Kwararraun Likitocin Tiyata 6 Ne Kacal Suka Rage A Kano – Farfesa Sani
- Aikin Hajji: Za A Fara Jigilar Alhazan Jihar Kwara A Ranar 12 Ga Watan Mayu
Sarkin Yashikira, Alhaji Umoru Sariki, ya tabbatar da harin. Ya bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen ƙarfe 6 na safe har zuwa 11, inda suka kashe mutum 1 tare da ƙona gidaje.
“Muna buƙaci gwamnati ta kafa sansanin Soja a yankin don kare mutane,” in ji Sarkin.
Wakilin Sojoji na barikin Sobi, Laftanar Stephen Nwankwo, ya tabbatar da cewa wani ɗan sandan gida ne aka kashe yayin da yake taimaka wa Sojojin. Maharan sun gudu lokacin da suka ga Sojoji sun iso.
Wannan sabon harin ya sake nuna buƙatar ƙarin matakan tsaro a yankunan kan iyaka.














