Wasu ‘yan bindiga sun farmaki gidan Alhaji Yusha’u Ma’aruf, mamallakin wani asibiti mai zaman kansa, a garin Zakirai da ke ƙaramar hukumar Gabasawa a jihar Kano, inda suka sace wani matashi mai shekaru 20 tare da jikkata ɗan uwansa.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan uku ɗauke da bindigogi da adduna sun afka wa gidan da misalin ƙarfe 2:15 na dare, suka sare yatsan hannun Abubakar Yusha’u mai shekaru 23 sannan suka sace ɗan uwansa, Mohammed Bello Yusha’u.
Daily Trust ta ruwaito cewa, sun kwashe wayoyi da kuɗaɗe kafin su tsere.
- Tinubu Ya Buƙaci A Mayar Wa BUK Filin Rimin Zakara Da Ake Taƙaddama A Kai
- Ɗan Uwan Gwamnan Kano Da Malaman NNPP Sun Koma APC
Kakakin rundunar ‘yansandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro sun fara bincike don ceto wanda aka sace da kuma kamo waɗanda suka aikata harin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp