Ƴan bindiga daga Mali sun kashe Manoma takwas tare da kwashe dabbobi 1,260 a yankin ƙaramar hukumar Gudu ta jihar Sokoto a ranar Juma’a. Ƴan bindigar, waɗanda suka shigo Nijeriya daga Mali, sun sace shanu 260 da tumaki da awaki 1,000 daga al’ummomin yankin.
A cewar Alhaji Umar Maikano Balle, Shugaban ƙaramar hukumar Gudu, ƴan bindigar sun yi ƙoƙarin lalata bututun mai a Jamhuriyar Nijar amma jami’an tsaro na Nijar suka hana su, wanda hakan ya sa suka kai hari kan manoman.
- Gwamnatin Kebbi Ta Ƙaddamar Rabon Taki Ga Manoma 48,000 Kyauta
- An Yi Garkuwa Da Sarkin Gobir Da Wasu Mutane 5 A Sokoto
Balle ya bayyana cewa jami’an tsaro sun samu labarin ƴan bindigar suna cikin wani daji a Gudu. Duk da ƙoƙarin fatattakar ƴan bindigar, ruwan sama mai yawa kamar da bakin ƙwarya ya hana motar jami’an tsaro kai ɗauki, wanda ya bai wa yan bindigar damar tserewa. Maharan sun kuma kai hari a ƙauyen Ƙarfen Sarki, inda suka kashe manoma takwas, ciki har da mambobi biyar na tsaron Al’umma a Sokoto da mazauna ƙauyen uku.
Wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan harin ke faruwa ba, domin yan bindiga daga Mali sun sha kai hari a baya. Balle ya jaddada barazanar da waɗannan ƴan bindiga ke yi, waɗanda ke amfani da iyakar da ke tsakanin Nijar da Najeriya wajen satar dabbobi da tayar da hankalin al’umma.