• English
  • Business News
Thursday, July 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 24 A Katsina

by Abubakar Sulaiman
3 weeks ago
in Labarai
0
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 24 A Katsina
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A ƙalla mutane 24 sun mutu a hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a ƙananan hukumomin Kankara da Sabuwa na jihar Katsina cikin mako guda. Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da manoma 20, mazauna uku, da wani Bijilantin guda.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kai hari a ƙauyuka kamar Yargoje, Kwakware, da Marmara, inda suka kashe mutane, suka sace wasu, tare da sace dabbobin gida. A wani hari a ƙauyen Marmara, ‘yan bindiga sun kashe ɗan Bijilanti (Civilian JTF) kuma sun jikkata wasu Civilian JTF biyu.

  • An Kashe Wasu ‘Yan Bindiga 12, An Kwato Makamai A Katsina
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaro 4 Da Manoma A Katsina

A ranar 18 ga Yuni, Ƴansandan Katsina sun ce sun ceto mata uku da wata yarinya ‘yar shekara ɗaya a yunƙurin sace su da aka yi a ƙauyen Mazare. Sun kuma jikkata mazauna biyu yayin da suka yi artabu da maharan.

Wani mazaunin Kankara ya danganta ƙaruwar hare-haren da rashin daidaiton yarjejeniyar zaman lafiya a yankin. “Idan aka yi sulhu a wasu wuraren kuma a wasu ba’a yi ba, ‘yan bindiga za su ci gaba da kai hare-hare,” in ji majiyyar.

Hukumar ‘yansandan ta tabbatar da cewa waɗanda aka ceto ba su ji rauni ba, yayin da waɗanda aka jikkata ke ci gaba da samun kulawa a asibiti. Jihar Katsina ta kasance ɗaya daga cikin jihohin da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga akai-akai.

Labarai Masu Nasaba

An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano

Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BanditsKatsinaPolice
ShareTweetSendShare
Previous Post

NDLEA Ta Kai Samame Fitattun Wuraren Shaye-shaye, Ta Cafke Mutane 19 A Kano

Next Post

Sin Za Ta Hanzarta Duba Bukatun Samun Lasisin Fitar Da Ma’adanan “Rare Earth” Zuwa Ketare

Related

An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano
Labarai

An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano

15 minutes ago
Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta
Labarai

Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta

2 hours ago
Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin

3 hours ago
EFCC Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Ɓullar Sabbin Hanyoyin Damfarar Kuɗi
Labarai

EFCC Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Ɓullar Sabbin Hanyoyin Damfarar Kuɗi

4 hours ago
Dangote Ya Yaba Wa Tinubu Kan Samar Da Ababen More Rayuwa A Nijeriya
Labarai

Dangote Ya Yaba Wa Tinubu Kan Samar Da Ababen More Rayuwa A Nijeriya

6 hours ago
Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Okpebholo A Matsayin Zaɓaɓɓen Gwamnan Edo
Da ɗumi-ɗuminsa

Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Okpebholo A Matsayin Zaɓaɓɓen Gwamnan Edo

8 hours ago
Next Post
Sin Za Ta Hanzarta Duba Bukatun Samun Lasisin Fitar Da Ma’adanan “Rare Earth” Zuwa Ketare

Sin Za Ta Hanzarta Duba Bukatun Samun Lasisin Fitar Da Ma’adanan “Rare Earth” Zuwa Ketare

LABARAI MASU NASABA

An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano

An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano

July 10, 2025
Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam

July 10, 2025
Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta

Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta

July 10, 2025
An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing

An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing

July 10, 2025
Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin

Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin

July 10, 2025
EFCC Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Ɓullar Sabbin Hanyoyin Damfarar Kuɗi

EFCC Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Ɓullar Sabbin Hanyoyin Damfarar Kuɗi

July 10, 2025
Dangote Ya Yaba Wa Tinubu Kan Samar Da Ababen More Rayuwa A Nijeriya

Dangote Ya Yaba Wa Tinubu Kan Samar Da Ababen More Rayuwa A Nijeriya

July 10, 2025
Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Okpebholo A Matsayin Zaɓaɓɓen Gwamnan Edo

Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Okpebholo A Matsayin Zaɓaɓɓen Gwamnan Edo

July 10, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

‘Yansanda Sun Kama Mutum 22 Kan Zargin Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu Suna Taimaka Wa Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya — Minista

Sauye-sauyen Tinubu Suna Taimaka Wa Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.