Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace Hakimin Birbyang, Alhaji Zubairu Garba, tare da wasu mata biyu a daren Lahadi a ƙaramar hukumar Kanam ta Jihar Filato. Rahotanni sun ce ƴan bindigar sun shigo ƙauyen ne da tsakar dare, suna harbi a iska kafin daga bisani su yi awon gaba da mutanen. Matar hakimin, wadda aka yi garkuwa da ita a farkon harin, ta samu damar tserewa daga hannun masu garkuwa.
Wannan lamari na baya-bayan nan ya biyo bayan sace-shi-da-kashe wa da aka yi wa Dagacin Shuwaka a yankin Kyaram, wanda shi ma ke cikin ƙaramar hukumar Kanam, mako guda kacal da ya gabata. Hakan ya ƙara tayar da hankali a tsakanin al’ummar yankin kan yawaitar hare-haren ƴan bindiga.
- Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato
- Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato
Ƙungiyar Cigaban Kanam (KADA), ta bakin shugaban ta Shehu Kanam da sakataren ta, Barista Garba Aliyu, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai a Jos. Sun ce harin ya auku ne misalin ƙarfe 1 na dare, inda ƴan bindigar suka yi awon gaba da hakimin zuwa wani wuri da ba a sani ba. Sun kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ceto waɗanda aka sace tare da dawo da zaman lafiya a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa garkuwa da mutane da hare-haren ƴan bindiga sun zama ruwan dare a yankin Kanam, inda mafi yawan waɗanda aka sace ake neman kuɗin fansa, yayin da wasu kuma ake hallaka su. Sai dai Daily Trust ya rawaito cewa, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Filato, DSP Alabo Alfred, bai amsa tambayar wakilinta ba a lokacin da ake rubuta wannan rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp