Ƴan ta’adda sun kai hari a ƙauyen Wake da ke ƙaramar hukumar Kachia, jihar Kaduna, inda suka kashe mutum takwas tare da yin garkuwa da wasu da dama.
Bayanan farko sun nuna cewa waɗanda suka samu raunuka a harin an garzaya da su Asibitin Katolika na Saint Gerard domin samun kulawar likitoci.
- Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Haifar Da Da Mai Ido A Katsina
- Gwamnatin Katsina Za Ta Sayo Babura 700 da Motoci 20 Don Samar Da Tsaro
Duk da cewa cikakkun bayanai kan lamarin ba su fito fili ba tukunna, majiyoyi sun tabbatar da faruwar harin. Sai dai duk wani yunƙuri na jin ta bakin jami’an ƙaramar hukumar Kachia bai samu nasara ba, domin sun ce za su yi ƙarin bayani bayan an kammala kula da waɗanda suka jikkata.
Karin bayani zai biyo baya…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp