Wasu da ake zargin ’yan Boko Haram/ISWAP ne sun saki mutum 11 daga cikin 14 da suka sace a kauyen Shawaram, yankin Doron Baga na karamar hukumar Kukawa a Jihar Borno. Wadanda aka sace sun hada da mata da yara.
A baya-bayan nan, LEADERSHIP ta ruwaito cewa ’yan ta’adda sun kashe sama da manoma 40 a kauyen Dumba, wanda ke kusa da Doron Baga. Wani mutum da ya tsira daga wannan harin ya ce ’yan ta’addan sun hana noma a yankin kuma sun yi barazanar kashe duk wanda ya karya dokarsu.
Majiyar tsaro daga yankin ta bayyana cewa an sace mutanen ne ranar 13 ga Fabrairu, 2025, karkashin jagorancin kwamandan ’yan ta’adda mai suna Tar, wanda ke addabar manoma da masu kiwo a gefen tafkin Chadi.
Wani shugaban al’umma da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, bayan sace mutanen, an bukaci fansar kuɗi daga iyalansu. “An saki mutane 11 bayan an biya naira miliyan 1.4 da al’ummar garin suka tara,” in ji shi.
A cewarsa, har yanzu mutum 3 na hannun ’yan ta’addan, ciki har da wata mata da aka sace tare da mahaifinta. Matar tana can tare da ’yan ta’addan bayan da suka ƙi sakin mahaifinta.
Majiyar ta ce Tar ya sake gargadi cewa idan ba a biya kuɗin fansa ba, matar za a yi mata auren dole, sannan sauran da ke tsare za su fuskanci hukunci mai tsanani.
Har zuwa yanzu, ba a samu wata sanarwa daga dakarun sojin Nijeriya ko hukumomin tsaro a kan wannan lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp