Wani mummunan farmaki da ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai a yankin Tangaza na jihar Sokoto ya yi sanadiyar mutuwar jami’an tsaro na sako su 11 , yayin da wasu suka ɓace.
An fara samun rahoton kashe mutane biyu a ranar Juma’a, amma adadin ya ƙaru bayan da aka gano wasu gawarwaki 9. Ana tsammanin akwai wasu gawarwakin da ke cikin dajin Lakurawa, inda Sojoji da sauran jami’an tsaro ke ƙoƙarin gano su.
- Yaķi Da Lakurawa: Jirgin Sojoji Ya Yi Kuskuren Jefa Bama-bamai Akan Al’umma A Sakkwato
- Harin Lakurawa: Shugaban Karamar Hukuma Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Sokoto
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa: “Farmakin ya fara ne bayan da ƴan Bijilantin suka hana Lakurawan kai hari ƙauyen Magonho, wanda ya haifar zazzafar musayar wuta. ‘Yan bindiga kimanin 40 ne, ɗauke da makamai masu yawan gaske, suka zo a babura 20, sun sace dabbobi kafin su gudu.”
Sojojin da ke FOB Masallaci sun mayar da martani da sauri, inda Lakurawan suka saki wasu dabbobin da suka sace. Duk da haka, ‘yan bindigar sun sake komawa ƙauyen Magonho, suna harbe -harbe tare da ƙona wata tashar sadarwa ta MTN kafin su sake guduwa.
Kakakin ‘yansanda na jihar Sokoto, Ahmed Rufai, ya tabbatar da faruwar harin da ƙona tashar MTN, amma bai iya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba a lokacin da aka yi rahoton.
Yayin da ake ci gaba da bincike, hukumomi na ƙoƙarin gano waɗanda suka ɓace da kuma gano sauran gawarwakin waɗanda abin ya shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp