An rufe kasuwar musayar yan kwallo ta shekarar 2025 a manyan gasannin kwallon kafa 5 dake Turai, (Premier League, Serie A, LaLiga, Bundesliga da Ligue 1) a daren Litinin.
LEADERSHIP Hausa ta zakulo maku yadda ta kaya da wasu ‘yan wasan Nijeriya a kasuwar musamman a ranar da aka rufe, wasu sun canza kungiyoyi walau a matsayin dindindin ko a matsayin aro, yayin da wasu kuma suka ci gaba da zama tare da kungiyoyinsu na yanzu bayan sun rasa damar komawa wasu kungiyoyi kafin a rufe kasuwar musayar yan wasa a daren Litinin.
Samuel Chukwueze
Samuel Chukwueze ya bar Ac Milan zuwa kungiyar Fulham dake buga gasar Firimiya a ranar Litinin, dan wasan wanda aka bai wa riga mai lamba 19 a Fulham, ya bar kungiyar AC Milan ta Seria A domin ya kammala saka hannu a yarjejeniyar zaman aro na tsawon kakar wasa guda sukutum a Fulham din, dan wasan mai shekaru 26 zai iske abokan wasansa a Nijeriya Aled Iwobi da Calbin Bassey.
Bictor Boniface
Wani dan wasan da ya tafi zaman aro shi ne Bictor Boniface wanda ya bar Bayer Leberkusen ya koma Werder Bremen a matsayin aro na tsawon kaka guda a ranar da za a rufe cinikin yan wasa, dan wasan na Nijeriya ya saka hannu akan kwantiragin da zai sa ya zauna a Werder har zuwa watan Yuni na shekarar 2026, kungiyoyin biyu ne za su biya albashin Boniface.
Tolu Arokodare
Wolbes ta sanar da daukar Arokodare daga kungiyar KRC Genk ta kasar Belgium dake buga gasar Belgian Pro League a ranar karshe ta musayar yan wasa, dan wasan mai shekaru 24 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru hudu da kungiyar ta Firimiya tare da zabin karin shekara, Arokodare ya koma Wolbes ne bayan ya buga wasa mai ban shaawa a kungiyar Genk a kakar wasan da ta wuce, inda ya kare a matsayin dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar ta Belgium da kwallaye 21.
Wilfred Ndidi
Ndidi ya koma kungiyar Besiktas dake buga gasar Super Lig ta kasar Turkiyya daga Leicester City a farkon kasuwar musayar yan wasa, dan wasan na Nijeriya ya koma kungiyar ta Turkiyya ne kan kwantiragin shekaru uku a watan Agusta, an danganta dan wasan mai shekaru 28 da kungiyoyi da dama a Turai amma ya zabi komawa Besiktas.
Bictor Osimhen
Osimhen ya koma Galatasaray ne kan kwantiragin shekaru hudu daga Napoli a farkon wannan bazarar bayan da zakarun Super Lig na Turkiyya suka yanke shawarar biyan Yuro miliyan 75 domin daukarshi, Osimhen, wanda zai samu albashin Yuro miliyan 15 a duk shekara, tuni ya ci wa Galatasaray kwallaye biyu a kakar wasa ta bana, dan wasan na Nijeriya ya ci wa Galatasaray kwallaye 37 a dukkan wasannin da ya buga a bara.
Chidozie Awaziem
Mai tsaron bayan ya dawo Faransa daga MLS, inda ya bar Colorado Rapids ya koma Nantes kan kwantiragin shekaru uku.
Moses Simon
Simon ya kammala komawa kulob din Faransa dake buga gasar Ligue 1, Paris FC a farkon wannan bazara, dan wasan mai shekaru 29, ya koma Paris FC ne daga Nantes kan kwantiragin shekaru uku, kan kudi Yuro miliyan 7, dan wasan ya ci kwallaye takwas sannan ya taimaka wajen cin 10 a wasanni 32 da ya buga wa Nantes a bara.
Gift Orban
Dan wasan mai shekaru 22 ya bar Lyon zuwa Hoffenheim a kan Yuro miliyan 9 tare da karin kudi na Yuro miliyan 3, tuni dai ya bude asusunsa a kasar Jamus inda ya zura kwallo a raga a wasansa na farko da kungiyar inda aka tashi 2-2.
Dukkan wadannan yan wasa dake buga kwallo a kasashen Turai na daga cikin wadanda kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya Eric Chelle zai iya gayyata domin wakiltar Nijeriya a wasannin neman tikitin buga gasar Kofin Duniya da za a cigaba da bugawa a wannan watan na Satumba da ya kama, Osimhen, Moses Simon da Samuel Chukwuze na daga cikin yan wasan gaba da Nijeriya ke ji dasu a cikin tawagarta, hakazalika a lokuta da dama yan wasan sun sha fitar wa kasar kitse a wuta a wasanni masu muhimmanci.
Yayin da wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin Duniya na FIFA ke gabatowa mako mai zuwa, yana da muhimmanci wadannan yan wasan su kasance cikin natsuwa domin wakiltar Nijeriya a wadannan wasannin, tawagar Super Eagles ta Nijeriya za ta kara da takwarorinta na kasar Rwanda da Afirka ta Kudu a wannan watan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp