Rundunar ƴansandan Jihar Jigawa ta ce ta samu nasarar gano wata mota da aka sace, tare da cafke wani da ake zargi da aikata laifin, tare da cafke masu safarar ƙwayoyi a wasu ayyuka daban-daban a ƙoƙarinta na yaƙi da miyagun laifuka a faɗin jihar.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a ɗutse, babban birnin Jihar Jigawa, jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansandan jihar, SP Shi’isu Adam, ya ce motar da aka sace, ƙirar Kia Sorento mai lamba GWL 225 BB, an gano ta ne bayan wani aikin haɗin gwiwa da jami’an leƙen asiri suka gudanar.
“Wadanda suka saci motar ba a tantance su ba, sun sato motar a kasuwar Gujungu da ke ƙaramar Hukumar Taura a ranar 14 ga Yuli, 2025,” in ji sanarwar.
- Ƴansanda Sun Fara Bi Gida-Gida Don Ƙwato Kayan Da Aka Sace Yayin Zanga-Zanga A Kano
- Ƴansanda Sun Dakile Hari, Sun Ceto Mutane A Abuja
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Nan take ƴansandan suka tura tawagar jami’an tsaro daga sashin kula da sa ido na reshen Gujungu, inda suka shiga aikin tare da fara gudanar da bincike mai zurfi, gami da daukar matakin gaggawa, da kuma yin amfani da bayanan sirri na al’umma, an yi nasarar gano motar tare da cafke su a ƙauyen Kanya Babba da ke ƙaramar Hukumar Babura.
Sai dai PPRO na Jigawa ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun gudu ne bayan da suka samu labarin jami’an ƴansanda na biye da su, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin cafke su domin gurfanar da su a gaban kuliya. “Motar da aka ƙwato tun daga nan aka miƙa ta ga mai ita bayan an tabbatar da tasa ce,” in ji shi.
A wani samame kuma, ƴansanda sun kama wani da ake zargin barayin USB ne, tare da ƙwato kayayyakin da aka lalata, ciki har da wata mota da aka yi amfani da ita wajen gudanar da aikin ba bisa ƙa’ida ba, inda ya ƙara da cewa “an kama su ne biyo bayan bayanan sirri da aka samu a ranar 15 ga Yuli, 2025, da misalin ƙarfe 0300 na safe.”
Wanda ake zargin mai suna Abubakar Sadi mai shekaru 25 dan asalin Kofar Waika ta jihar Kano, an kama shi a wurin da lamarin ya faru, yayin da sauran wadanda ake zargin suka tsere cikin daji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp