Rundunar Ƴansandan jihar Yobe tare da haɗin gwuiwar ‘yan bijilanti sun bankaɗo maɓoyar masu garkuwa da mutane, inda suka ceto mutum biyu da aka sace tare da kwato bindiga ƙirar AK-47.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana cewa shalƙwatar ‘yansanda ta ƙaramar hukumar Gujba ta samu kiran gaggawa daga wani ganau a garin Buni Yadi da misalin ƙarfe 10 na safe ranar 25 ga Mayu, 2025.
Bayan samun kiran, Dungus ya ce ‘yansanda tare da goyon bayan al’umma sun gano maboyar ‘yan ta’addan, inda suka kai samame a wajen.
A yayin musayar wuta da ‘yan bindigar, waɗanda suka ji raunuka, suka tsere tare da barin waɗanda suka sace da kuma bindiga kirar AK-47 ɗauke da bindigu biyu da harsasai 25.
Dungus ya ce an ceto waɗanda aka sace ba tare da sun samu wata illa ba, kuma an kai su asibiti domin duba lafiyarsu, yayin da ake ƙoƙarin cafke waɗanda suka tsere domin gurfanar da su a gaban kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp