Rundunar ƴansandan jihar Filato ta kama wata mata mai suna Nanman Pungtel da yara uku da ba ta iya bayar da cikakken bayani kan yadda ta same su a unguwar Old Airport da ke Jos ba. Wannan na zuwa ne bayan samun wasu bayanan sirri da aka miƙa wa rundunar.
Bayan fara bincike an kama shugaban ƙungiyar, Pastor Dayo Bernard na cocin End Time Army Ministry, wanda ya amsa laifin yin garkuwa da yara 13 daga jihar, wanda ya sayar da su akan kuɗi tsakanin ₦350,000 zuwa ₦750,000. Haka kuma, an ceto yara biyar da aka yi garkuwa da su a yankin Kwande na Qua’anpan.
- ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Makiyaya Tare Da Kashe Shanu A Jihar Filato
- Ƴansanda Sun Kama Mutane 859, Sun Kwato Makamai 27 Da Alburusai 115 A Filato
Kwamishinar harkokin mata ta Filato, Panglang Dafur, ta yi Allah wadai da rawar da wasu shugabannin addini ke takawa wajen safarar yara. Reverend Dr. Amos Mohzo na COCIN ya yi kira ga iyaye da shugabannin addini su wayar da kan al’umma kan illar wannan mummunan aiki.
Gwamna Caleb Mutfwang ya yi gargaɗi kan masu aikata wannan ɗabi’a tare da alƙawarin ɗaukar matakan hukunci. Ya kuma yi kira ga iyaye su ɗauki nauyin kula da yaran su domin gujewa faɗawa hannun masu aikata laifi.