Hukumar Ƴasnanda ta Jihar Jigawa ta kama mutum huɗu, ciki har da wani ango, bayan rasuwar matarshi a ƙaramar hukumar Sule Tankarkar. Wannan lamari ya faru ne a daren Asabar, lokacin da jami’in ‘yansanda na ƙaramar hukumar Sule Tankarkar ya fara bincike kan zargin da ya shafi mijin da abokansa.
Mijin, Auwal Abdulwahab, mai shekaru 20, an zarge shi da haɗa kai da abokansa guda uku – Nura Basiru, Muttaka Lawan, da Hamisu Musa, dukkansu na ƙauyen Tungo – don tilasta wa matarsa yin jima’i, wanda ita kuma ba ta amince da su ba. A yayin ƙoƙarin hakan ta ƙarfin tsiya ta rasu.
- Gwamna Namadi Na Jihar Jigawa Ya Cancanci Karramawar LEADERSHIP – Hamisu Gumel
- Rashin Wutar Lantarki: Jihohin Kano, Katsina Da Jigawa Na Samun Wutar Awa 2 Ne Kacal A Kullum
Bayan samun rahoton, Ƴansanda sun garzaya zuwa wurin, inda suka ɗauki gawar matar zuwa Asibitin ƙwararru na Gumel, inda likita ya tabbatar da mutuwarta. An mika gawarta ga iyalanta domin yi mata jana’iza.
Hukumar ‘Yansanda ta bayyana cewa, waɗanda ake zargin na fuskantar tuhumar haɗin kai da kisan kai.
Kwamishinan ‘Yansanda, CP AT Abdullahi, ya umarci cewa a tura lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka na Jihar (SCID) a Dutse domin gudanar da cikakken bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp