Rundunar ƴansandan jihar Legas ta fara aiwatar da dokar da ta shafi amfani da gilashin mota mai duhu (tinted glass) a cikin jihar a ranar Alhamis. Wannan mataki na daga cikin shirin tabbatar da tsaro da bin ƙa’ida, tare da bin umarnin Sufeto Janar na ƴansanda, IGP Kayode Egbetokun.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abimbola Adebisi, ta bayyana cewa masu motoci da ba su da lasisin amfani da gilashin mota mai duhu dole ne su nemi izini ta hanyar shafin www.possap.gov.ng. Ta kuma ja hankalin masu motoci da ba sa son amfani da wannan lasisi su cire gilashin ko su maye gurbinsa da fari, bisa ga dokar ababen hawa (Prohibition of Tinted Glass) Act 2004.
- Yadda Ƴan Agbero’ Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Abuja
- ‘Yansanda Sun Ceto Wani Dan Shekara 25 Da Aka Sace A Jihar Kebbi
Rundunar ta yi gargaɗi cewa duk wata mota da aka kama da gilashi mai duhu ba tare da lasisi ba za a kwace ta, kuma a gurfanar da mai motar a gaban kotu. SP Adebisi ta kuma tunatar da masu ababen hawa cewa wannan aiki na cikin dokokin zirga-zirga da sauran ƙa’idojin tsaro da ake aiwatarwa a jihar.
Kwamishinan ƴansanda na jihar, CP Olohundare Jimoh, ya buƙaci jami’an da ke gudanar da aikin su gudanar da shi cikin mutuntawa da ƙwarewa, tare da tabbatar da kare ƴancin jama’a. Ya yi gargaɗin cewa duk jami’in da ya yi amfani da aikin wajen cutar da jama’a zai fuskanci hukunci, tare da mai kula da shi (supervisor).
CP Jimoh ya tabbatar wa jama’ar jihar Legas cewa aikin ba kawai don takura masu bin doka bane, sai don ƙara tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Rundunar ta kuma samar da lambobin waya da shafukan sada zumunta domin jama’a su riƙa kai rahoton duk wani jami’i da bai yi aiki yadda ya kamata ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp