• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴansanda Sun Gano  Ƙarin Bama-Bamai 9 Da Basu Fashe Ba A Kano

by Abubakar Sulaiman
4 months ago
Kano

Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta tabbatar da gano bama-bamai tara da basu fashe ba (UXOs) a wurin da fashewar da ta yi sanadin mutuwar mutane biyar ta faru a Kamfanin Yongxing Steel da ke unguwar Mariri a kan titin Ring Road.

Fashewar da ta faru da karfe 11:30 na safe ranar 21 ga watan Yuni ta kashe mutane biyar tare da jikkata wasu da dama.

  • Abba Ya Dace Ya Zama Gwamnan Kano Na Har Abada Ba Shekaru 8 Kaɗai Ba – Arch Ali Hassan
  • Mun Gano Wurare 52 Da Ake Aikata Laifuka A Kano – Janar Mai Adda’u

Mai magana da yawun Ƴansandan jihar, DSP Hussaini Abdullahi, ya bayyana cewa binciken da sashin EOD-CBRN ya gudanar ya nuna cewa fashewar ta faru ne sakamakon wani bam da aka yi amfani da shi a yaƙi (UXO) wanda ya fashe ba da gangan ba yayin sauke tarkacen karafa.

“Binciken ya nuna cewa fashewar ta fito ne daga wani bam da aka yi amfani da shi a yaƙi (UXO), ba wanda aka kera da hannu (IED) kamar yadda aka fara zato ba,” in ji sanarwar. “An gano bama-bamai tara iri ɗaya daga wurin.”

Kwamishinan Ƴansandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma yi fatan waɗanda suka jikkata da su samu sauki.

Ƴansandan sun kuma yi kira ga jama’a da su nuna fahimta, suna masu cewa babu wata barazana ta tsaro a halin yanzu, kuma sun nemi da a kai rahoton duk wani abu ko aiki da ake zargi.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus
Manyan Labarai

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya
Da ɗumi-ɗuminsa

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

October 18, 2025
Next Post
Binciken CGTN: Masu Bayyana Ra’ayoyi Na Kasa Da Kasa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Amurka Kan Iran

Binciken CGTN: Masu Bayyana Ra’ayoyi Na Kasa Da Kasa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Amurka Kan Iran

LABARAI MASU NASABA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

October 19, 2025
Yadda Ake Alkaki

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.