A safiyar Juma’a, jami’an tsaro sun toshe fadar Sarki a Kano sannan a wani yunƙuri na hana Sarki Muhammadu Sanusi II halartar wani taron sarauta a Bichi, cikin jihar Kano.
Wannan labarin ya fara fitowa ne daga wata kafar watsa labarai ta intanet, News Point Nigeria, wanda aka ambaci wata majiya daga cikin masarautar cewa Sarki Sanusi II ya shirya halartar taron naɗin sabon Hakimin Bichi. Sai dai, jami’an tsaro riƙe da makamai sun buƙaci Sarki Sanusi II ya zauna a cikin fadar yayin da aka toshe ƙofar fadar da motocin ɗaukar dakarun Sojoji.
Har ila yau, wata majiyar daga gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusif, ya tura wata tawaga zuwa fadar, amma ita ma aka hana su shiga.