Hukumar ‘Yansanda ta Nijeriya (NPF) ta janye gayyatar da ta yi wa Sarki Sanusi II dangane da abin da ya faru a Jihar Kano yayin bikin Sallah na 30 ga Maris, 2025. An miƙa gayyatar ne domin baiwa Sarkin damar bayar da bayanin yadda aka yi wani ya rasa ransa.
Sai dai, bisa shawarwari daga masu ruwa da tsaki da kuma bisa ga ƙudirin Shugaban hukumar Ƴansanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, na tabbatar da cewa siyasa bata shiga cikin ayyukan Ƴansanda ba ko a yi musu fassara ta kuskure, an umarci a janye gayyatar.
- Ƴansanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ɗan Bijilanti A Tawagar Sarki Sunusi II
- Ka Cire Sarkin Kano Bayero Daga Fadar Nasarawa – Gwamnatin Kano Ga Tinubu
A maimakon haka, an umarci ma’aikatan sashen binciken sirri na ‘Yansanda (FID) su tafi zuwa Kano domin tattaro bayanin Sarki Sanusi, bisa ga umarnin IGP.
Kafin bukukuwan Sallah, bayanan sirri daga ‘Yansanda sun nuna cewa Sarakuna biyu da ke ta ƙaddama a Jihar Kano, Alhaji Ado Bayero da Sunusi Lamido Sanusi II – suna shirin gudanar da bukukuwan hawan Sallah. IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya tura DIG mai lura da Arewa maso Yamma, DIG Abubakar Sadiq, domin shiga tattaunawa da masarautun da gwamnatin Kano. An amince cewa babu hawan Sallah da za a gudanar domin kiyaye zaman lafiya da tsaro a cikin al’umma.
Duk da wannan yarjejeniya, Sarki Sanusi, wanda ya halarci Sallar idi cikin mota, ya yanke shawarar hawa doki a cikin wata al’ada bayan Sallar idi, tare da taimakon matakan jami’an tsaro na Bijilanti.
Wannan ya haifar da wani rikici, wanda ya jawo mutuwar Usman Sagiru da raunata wasu da dama. Wannan shi ne abin da ‘Yansanda suka yi ƙoƙarin hana faruwa, kuma sun ɗauki matakan gaggawa bayan wannan al’amari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp