Hukumar Ƴansandan Jihar Kano ta kama mutane 33 da ake zargin ‘yan daba ne yayin wani sintirin aiki na tsawon kwanaki biyar wanda aka gudanar domin kakkaɓe masu aikata mummunan aiki a cikin birnin Kano.
Kakakin rundunar ‘Yansandan Jihar, SP Abdullahi Kiyawa, wanda ya fitar da wannan sanarwa, ya bayyana cewa an kama mutanen ne tsakanin 23 ga Afrilu zuwa 28 ga Afrilu, 2025, yayin da ake gudanar da kame a wuraren da aka gano ɓata gari na shan bidirinsu.
- Ƴansanda Sun Janye Gayyatar Sarki Sunusi, Zasu Zo Kano Da Kansu
- Hukumar Shari’a Ta Dakatar Da Magatakarda 2, Ta Kuma Gargaɗi Alƙalai 2 A Kano
Kiyawa ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne ta hannun jami’ai na musamman wanda ke ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ‘Yansandan Jihar, CP Ibrahim Bakori, da kuma shugabancin CSP Bashir Gwadabe na sashin yaƙi da daba.
Daga cikin kayan da aka samu daga a hannun waɗanda aka kama akwai makamai masu hatsari, da kwayoyi marasa izini, da dukiyoyin mutane da aka sace.
An bayyana cewa waɗanda aka kama za su fuskanci tuhuma kan laifukan sata, da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma laifukan da suka shafi shaye-shayen kwayoyi.
CP Bakori ya gode wa al’ummar Kano saboda goyon bayan da suke ba su a ƙoƙarin su na yaƙar masu aikata laifuka tare da kira ga ci gaba da haɗin kai wajen kai rahoton abubuwan da suke zargi ga Ƴansanda.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp