Rundunar Ƴansanda ta Jihar Kano ta cafke ƴan wata ƙungiya masu damfara mutane ta hanyar yin sojan gona a matsayin jami’an tsaro domin karɓar kuɗi daga hannun mutane a Kano, da Kaduna da Katsina. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a ranar Asabar, inda ya ce jami’an sun kama mambobin ƙungiyar guda biyar ne bayan samun sahihin bayanan leƙen asiri.
Kiyawa ya bayyana sunayen waɗanda aka kama da suka haɗa da Aliyu Abbas (35), da Sani Iliyasu (47), da Ashiru Sule (41), da Abubakar Yahaya (45), da Adamu Kalilu (45). An cafke su ne da ƙarfe 1:00 na rana a ranar Alhamis, 16 ga Oktoba, 2025, ta tawagar Special Intervention Squad (SIS) yayin da suke yin cikakkiyar shiga irinta jami’an ƴansanda.
- Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja
- Kotu Ta Ɗaure Mai Horas Da ‘Yan Wasa Shekaru 8 Sakamakon Zargin Luwaɗi Da Ƙaramin Yaro A Kano
A cewar Kiyawa, an kwato daga hannunsu takardar bogi ta ƴansanda, da ankwa, da Kudin CFA 2,500, da wasu takardun kuɗin Naira da aka lalata, da motar aiki ƙirar Peugeot 406 mai launin shuɗi mai lambar NSR-188-BD. Ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu na yin amfani da takardar bogi wajen damfarar jama’a a jihohin uku.
Kwamishinan Ƴansanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar ba za ta lamunci irin wannan Sojan gona ko harkar damfara ba, inda ya tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da duk wani motsi ko mutane da ake shakku a yankunansu tare da sanar da ofishin ƴansanda mafi kusa don kare rayuka da dukiyoyi.