Jami’an rundunar ƴansanda ta jihar Nasarawa sun samu nasarar cafke wani shahararren shugaban ƴan fashi da masu garkuwa da mutane, Mohammed Bammi wanda aka fi sani da Zomo, tare da wasu abokan aikinsa a yayin wani babban sumamen da suka kai kan miyagu a jihar.
Rundunar ta bayyana cewa Zomo ya daɗe yana jagorantar garkuwa da mutane da fashi a yankin ƙaramar hukumar Doma da kewaye. An cafke shi ne yayin wani sumamen tsaftace dajin Doka da jami’an sashin Doma suka gudanar, bayan ya tsere a watan Yuli. An ce ya yi yunƙurin kai wa jami’an hari da wuka lokacin da za a damƙe shi, amma aka rutsa shi aka kama shi da ransa.
- Sanusi II Ya Gudanar Da Hawan Nassarawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda A Kano
- Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Aminu Ado Bayero Na Gyaran Fadar Nassarawa
Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya ce bincike ya kai jami’an zuwa maɓoyar Zomo a ƙauyen Alagye, Doma, inda suka gano makaman da suka haɗa da bindigar Pump Action, da bindigar AK-47 da aka haɗa ta a gida tare da mazaganya, da harsasai guda biyu da alburusai guda biyar, da wuka, da igiya, da wayoyi biyu, da kuma kayan sanya wa na jami’an NSCDC.
Haka kuma, Nansel ya ce jami’an rundunar Awe sun cafke wasu mutane biyar da ke cikin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane 10 bayan samun sahihan bayanai. An kama su ne a ƙauyen Gidan Taku. Waɗanda aka cafke sun haɗa da Michael Ato, da Richard Ato, da Alom Bernard, da Hangior Ato da Jacob Hunde (wanda aka fi sani da Okocha). An kwace bindigogi biyu na AK-47 da aka yi a gida da harsashi guda daya daga hannunsu.
Kakakin ya ƙara da cewa bincike ya gano cewa a watan Afrilu 2024 wannan ƙungiya ta taɓa sace mijin Blessing John, mai suna John Ada Kuje, inda suka karɓi kuɗin fansa kafin su sake shi. Kwamishinan ƴansanda na jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya jinjinawa jami’an bisa kwazo da sadaukarwa tare da jan hankalinsu da su ci gaba da matsa lamba har sai an kawar da masu garkuwa da mutane da ƴan fashi a jihar. Duk waɗanda aka kama an mika su ga sashi na musamman na masu garkuwa da mutane domin ƙarin bincike da gurfanarwa a kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp