Rundunar ‘Yansandan Jihar Yobe ta kama wata mata mai shekaru 54, bisa zargin safarar alburusai guda 350 masu girman 7.62×39mm.
An kama ta ne yayin da take jigilar alburusan daga Buni Yadi zuwa Damaturu.
- Kwanaki Kaɗan Bayan Harin Ta’addanci A Mafa, ‘Yan Ta’adda Sun Sake Kai Wani Harin A Yobe
- Ambaliya: Gwamnatin Yobe Za Ta Tallafa Wa Mutane 25,500 Da Naira Biliyan 1.4
DSP Dungus Abdulkarim, mai magana da yawun rundunar, ya bayyana cewa kama matar ya biyo samun bayanan sirri ne, wanda ya kai ga jami’an Ƴansanda a Damaturu daƙile wata mota ƙirar Golf 3 inda aka ɓoye alburusan a cikin kayanta.
Ana ci gaba da bincike kan wannan zargi tare da neman gano masu hannu a wannan aika-aika.
Kwamishinan ‘Yansanda, Garba Ahmed, ya buƙaci al’umma da su kasance masu sa ido tare da kai rahoton duk wani abin da ba su gane ba ga hukumomin tsaro.