Ƴansandan sun yi nasarar kai hari kan sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Benue da Delta, inda suka kashe mutane uku, suka ceto waɗanda aka sace biyu, tare da kama wasu tara. A Benue, waɗanda ake zargi da shirya hare-hare kan jami’an tsaro sun samu raunuka masu tsanani bayan wata musayar wuta da kusa da Tse-Gondo, inda aka kwato bindigogi biyu da ƙirar gida da wasu harsasai.
A Delta, Ƴansandan sun kama Henry Okpor da ake zargi da sace motoci a ranar 22 ga Afrilu, inda suka kwato bindiga ɗaya da motoci biyu. Kwanaki uku bayan haka, wata tawaga ta musamman ta kama wasu ‘yan daba biyu na ƙungiyar Vikings, inda suka kwato bindigogi biyu da harsasai biyar.
- CDD Ta Soki NBC Kan Cin Tarar Trust TV Da Wasu Miliyan 20
- Gwamnan California: California Za Ta Ci Gaba Da Bude Kofa Ga Sin Domin Gudanar Da Kasuwanci
An yi bata kashi a wani iftila’in garkuwa da mutane a Agbarho lokacin da ‘yan sanda suka ceto waɗanda aka sace biyu bayan wata gwagwarmaya a dajin Uvwiama na Ughelli ta Arewa. An kama mutane tara a wannan artabun, tare da kwato bindigogi da dama.
Kakakin ‘yansanda ACP Olumuyiwa Adejobi ya yaba da jajircewar jami’an tsaro, yana mai cewa nasarorin da aka samu sun nuna irin gudunmawar da ‘yansandan Nijeriya ke bayarwa wajen yaki da laifuka a faɗin ƙasar. Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da rahoton duk wani abin da zai iya taimakawa wajen warware matsalolin tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp