Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta dakile wani yunkurin satan mutane tare da ceto mutum 13 daga hanun masu garkuwa da mutane a garin Maibakko da ke karamar hukumar Sabuwa.
Bayanin haka na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jam’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadik Aliyu, ya raba wa manema labarai.
- Mutum Biyu Sun Faɗa Komar ‘Yansanda Bisa Zargin Sata A Gombe
- Hare-haren ‘Yan Bindiga A Sahel Sun Jefa Shugabannin Soji Cikin Zulumi
Kamar yadda sanarwar ta ce, a ranar 6 ga watan Fabrairun wannan shekarar, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a garin Maibakko, inda suka yi garkuwa da wasu mutanen garin.
A cewar sanarwar, jami’an tsaro sun garzaya domin kai dauki, inda suka dakile harin tare da ceto mutum 13. Sai dai sanarwar ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun harbe mutum biyu har lahira, tare da jikkata wani mutum daya.
Sanarwar ta ce an kama mutum biyar dauke da tarin wayoyin lantarki da aka sata, yayin da wasu biyu daga cikin abokan aikinsu suka tsere.
DPS Abubakar ya ce kwamishinan ‘yansandar jihar, CP Aliyu Abubakar Musa, ya gode wa babban sufeton ‘yansanda, Kayode Egbetokun da Gwamna Dikko Radda saboda goyon bayan da suke bayarwa wajen karfafa tsaro.