Hukumar Ƴansanda a birnin Tripoli, Libya, ta kama wasu ƴan Nijeriya biyu bisa zargin hannu a wasu jerin fashin shagunan kasuwanci da ake gudanarwa a sassan birnin.
Rahotanni sun bayyana cewa an cafke mutanen ne a ranar 25 ga Agusta 2025, bayan wani bidiyon na’urar tsaro ya nuna su suna satar kaya daga wani shago. An ce dukkansu ba su da takardun izinin zama a ƙasar.
- Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya
- Yadda Aka Cafke Masu Saka Ƙwayoyi A Jakunkunan Matafiya A Filin Jirgin Sama A Kano
Ƙungiyar Migrant Rescue Watch, wadda ke sa ido kan al’amuran baƙi da ƴan gudun hijira a Libya, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata. Ta ce: “’Ƴansanda a Tripoli sun kama ƴan gudun hijira biyu daga Nijeriya bisa laifin shiga da kuma fashi a shagunan kasuwanci domin karɓe kuɗi. An miƙa su ga ofishin mai gabatar da ƙara.”
Hukumomi sun yi imanin cewa waɗanda ake zargin na da alaƙa da wasu fasa shaguna da dama a cikin birnin, kuma yanzu haka an miƙa su ga mai gabatar da ƙara domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da su a kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp