Wasu matasa biyu a ƙaramar hukumar Sagbama ta jihar Bayelsa, sun gamu da ajalinsu yayin da suke yunƙurin sace fitulun kan titi masu amfani da hasken rana.
Kamar yadda Gidan Rediyon Tarayya (FRCN) ya rawaito, an gano gawarwakin mutanen ne a safiyar yau Litinin, Inda wani shaidar ganau ya bayyana cewa, waɗanda ake zargin sun gamu da ajalinsu ne bayan sun cire fitulu huɗu sun ajiye a ƙasa, suna ƙoƙarin cire ta biyar inda sandar ta fado kan wayoyin wutar lantarkin.
- Nijeriya Ta Samu Sama da N181bn Daga Wutar Lantarkin Da Ta Sayarwa Kasashen Waje
- Sin Na Matukar Adawa Da Binciken Da Amurka Ta Yi Kan Manufofin Sana’o’in Na’urorin Lantarki Na Kasar Sin
Ya ce kasancewar akwai wutar lantarki a lokaci sai ta ja su, inda ɗaya daga ciki ya babbake sosai tare da mutuwa nan take, ɗayan kuma ya ƙone ƙurmus har ba a iya gane shi.
Duba da yadda satar fitilun kan tituna ya yi ƙamari a yankin, mazauna garin sun bayyana fatan wataƙila abin da ya faru zai zamo izini ga sauran mutane masu aikata makamancin hakan don su tuba su daina.