Akalla mutane 10 ne suka jikkata yayin da ‘yansanda suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa bata-gari da suka kutsa cikin masu zanga-zangar #EndBadGovernance a ranar Alhamis a fadin jihar Jigawa.
Jihar Jigawa ta fuskanci wani yanayi wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin jihar yayin da zanga-zangar adawa da kuncin rayuwa da yunwa ta kunno kai a fadin jihar wacce ta mamaye manyan garuruwa 10 da ke fadin jihar.
An samu rahotannin barna tare da wawushe dukiyoyin gwgwamnata yayin gudanar da zanga-zangar.
Rahoto daga birnin Hadejia ya tabbatar da cewa, an kwantar da mutane hudu a wani asibiti sakamakon raunuka da shakar barkonon tsohuwa da jami’an ‘yansandan yaki da tarzoma suka harba, yayin da aka balle tare da wawushe kayayyakin noma mallakar gwamnati a yankin.
A garin Gumel ma an samu makamancin hakan, inda aka wawure kayayyakin noma na hukumar sayar da kayayyakin noma ta jihar Jigawa (JASCO), kuma an fasa wani gida mallakin dan majalisar wakilai, mai wakiltar mazabar Gumel, Gagarawa, Maigarati a majalisar tarayya a jihar da kuma ofishin jam’iyyar APC mai mulki da ke yankin.
A garin Birnin Kudu, shagunan sayar da taki da hatsi na jihar duk an wawushe su, yayin da bata-garin suka tare duk wasu manyan hanyoyin da suka hada garin Kano zuwa Maiduguri.
A Dutse, babban birnin jihar, an kai mutane biyar babban asibitin Rasheed Shekoni sakamakon raunukan da suka samu, yayin da jami’an tsaro suka yi nasarar hana bata-garin barna da wawushe dukiyoyin jama’a. Sai dai an kona babbar sakatariyar jam’iyyar APC ta jihar.
Hakazalika a garuruwan Jahun, Kazaure da Shuwarin, al’amarin duk iri daya ne kamar yadda ya gudana a garuruwan da muka ambata a baya.