An samu koma baya a yunkurin dawo da wutar lantarki a yankin Arewa maso Gabas, yayin da ɓata-gari suka sake lalata wasu hasumiya guda uku da ke kan layin Biu zuwa Damboa tare da yin awon gaba da wasu kayan aikin.
Kazalika sun lalata wata hasumiyar lantarkin da ke kan layin Makurdi zuwa Jos tare da cire wasu sassan kayan da ke jiki.
Cikin wata sanarwa da Kamfanin samar da wutar lantarki na kasa (TCN) ya fitar, ya kara da cewa daya daga cikin sabbin husumiyoyin lantarki hudu da aka sake kafawa da ke kan layin sadarwa na Jos zuwa Gombe ya ruguje a lokacin aikin daura igiyar waya.
Kamfanin TCN ya yi nadamar lamarin da ya faru a yayin wanda dan kwangilar kokarin daura igiyar wayar lantarkin a hasumiya ta karshe don cika wa’adin ranar 27 ga Mayu na dawo da wutar lantarkin a Arewa maso Gabas.